12 Yuli 2026 - 18:40
Source: Al-Mayadeen
Iran: A Mataki Uku A Jere Ta Kai Hari A Kan Sansanoni Da Cibiyoyin Amurka Martani Ga Ta'addancin Amurka

A martani ga ta'addancin Amurka da ya shafi ƙasar, sojojin Iran da dakarun juyin musulunci sun kai hari a kan sansanoni da cibiyoyin Amurka a yankin.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Dakarun juyin musulunci na Iran, a yau Lahadi, sun sanar da lalata cibiyar jagoranci da sarrafawa da rumfunan ajiye jiragen leken asiri nau'in "MQ9" a sansanin "Amir Hassan" na Amurka a Jordan da makamai masu linzami na ballastic, a matsayin martani ga ta'addancin Amurka da ya shafi ƙasarta a daren Asabar zuwa Lahadi.

Dakarun juyin musulunci a cikin wata sanarwa sun tabbatar da dakatar da ƙoƙarin tsarin Amurka na "ƙirƙirar hanyar da ba ta dace ba a kudancin mashigar Hurmuz," da martani mai ƙarfi, suna nuni da cewa Washington tana ƙoƙarin "tilasta nufinta ta a kan gwamnatin Oman."

Iran: Ci Gaba Da Ta'addanci Zai Haifar Da Martani Mafi Tsanani

Dakarun juyin musulunci sun ɗauki harin Amurka na shammaci a kan wasu sansanonin bakin teku da hasumiyoyin sadarwa a bakin tekun kudu, a matsayin ƙoƙari na "huce haushin rashin nasararta."

Don haka, sun tabbatar da cewa mayakan sojojin sama na dakarun juyin musulunci sun kai hari a kan sansanonin soji na Amurka, suna bayyana cewa matakin farko na martani ya haɗa da kai hari a kan ababen more rayuwa da cibiyoyin soji a sansanin sojan sama na "Amir Hassan" a Jordan.

Dakarun juyin musulunci a ƙarshen sanarwarsu sun jaddada cewa ci gaba da ta'addancin Amurka zai haifar da "martani mafi tsanani."

Mataki Na Biyu Na Martani

A mataki na biyu na martani, dakarun juyin musulunci sun sanar da kai hari kan wani jirgin ruwan da ya shigo ba bisa ka'ida ba na biyu a mashigar Hurmuz da dakatar da shi, da kuma kai hari a kan cibiyoyi a sansanin "Al-Udeidah" a Qatar.

Ofishin hulda da jama'a na dakarun juyin musulunci a cikin wata sanarwa ya tabbatar da cewa an kai harin ne a matsayin martani ga ci gaba da ta'addancin sojojin Amurka a kan sansanonin bakin teku na sojojin Iran.

Sanarwar ta kara da cewa sansanin sojan sama na Amurka "Al-Udeid" a Qatar ya fuskanci harin makamai masu linzami na ballastic, wanda ya haifar da lalata cibiyar kula da jiragen yaƙi da cibiyar bayar da umarni da sarrafawa a sansanin.

Dakarun juyin musulunci sun tabbatar da cewa ci gaba da ta'addancin Amurka da yahudawa zasu  fuskance shi da "martani mafi tsanani da ƙarfi," suna ƙarkarewa da cewa: "In Kun Yaƙe Mu, Za Mu Yaƙe Ku."

Mataki Na Uku Na Martani

A mataki na uku, dakarun juyin musulunci sun sanar da lalata cibiyoyin tallafi na dabaru da cibiyoyin  ba da man fetur ga jiragen ruwan dakon jiragen sama na Amurka a tashar jiragen ruwa ta Duqm a Oman.

Ofishin hulda da jama'a na dakarun juyin musulunci a cikin wata sanarwa ta ce: "Lallae Karfin Iradar da ta bayyana a matakin al'ummar Iran ta ɗauka a yayin jana'izar da ba a taɓa yin irinsa ba, wadda miliyoyin mutane suka halarta kuma ta ba da mamaki ga duniya, a yau tana mai bayyana a cikin jarumtar da mayakanku suke yi."

A cikin bayani, mayakan sojojin sararin samaniya na dakarun juyin musulunci sun aiwatar da "Harin shammaci mai faɗi kai tsaye wanda ya kai hari a kan cibiyoyin daukin dabaru na jiragen ruwan yaƙi da cibiyoyin ba da man fetur ga jiragen ruwan dakon jiragen sama na Amurka a tashar jiragen ruwa ta Duqm a Sultanate Oman, wanda ya haifar da lalata su."

Sojojin Iran Sun Kai Hari A Kan Sansanonin Amurka A Bahrain Da Kuwait

A nasu bangaren, sojojin Iran sun kai hari a kan na’urar tsaron "Patriot" da ɗakin ajiyar makamai da wurin na’urar radar jiragen mara matuki ta sojojin Amurka a Kuwait,.

Kuma a Bahrain, sojojin sun kai hari a wani hari na daban da jiragen mara matuki a kan nau’arar sadarwa da wurin radar na sojojin Amurka.

Don haka, sojojin sun sanar da cewa sakamakon waɗannan motsin da rashin tsaro a yankin alhakinsu na kan yahudawa da Amurka ne, kuma idan aka maimaita waɗannan hare-haren, to "martaninmu zai fi tsanani."

A sakamakon haka, kamfanin dillancin labarai na "Tasnim" ya ba da rahoton kunna na’urar tsaron sama a Jordan, yana nakalto daga majiyoyi cewa wani harin makami mai linzami ya shafi manufofi da muradun Amurka a Kuwait, baya ga jin karar fashe-fashe a sansanonin Amurka a Bahrain.

A cikin wannan tsari, ma'aikatar cikin gida ta Bahrain ta sanar da kunna ƙararrawar faɗakarwa a ƙasar.

Bugu da kari, an ji karar fashe-fashe a babban birnin Qatar Doha, bayan labarai na farko game da karar fashe-fashe a UAE.

"Martanin Iran Kan Ta'addancin Amurka Yana Kafa Sabon Ma'auni, Yayin Da Mashigar Hurmuz Ke Zama Jigon Arangama A Cikin Rashin Ikon Washington Na Tilasta Sharuɗɗanta Ko Kawo Ƙarshen Rikicin"

Ta'addancin Amurka A Kan Iran

Cibiyar Rundunar Amurka ta sanar, a daren Asabar zuwa Lahadi, fara aiwatar da zagaye na uku na hare-haren da sojojinta ke kaiwa a kan Iran a cikin wannan mako, tana zargin cewa an kai su ne a matsayin martani ga kai hari da dakarun juyin musulunci suka yi wa jirgin dakon kwantena "GFS Galaxy," wanda ke ɗauke da tutar Cyprus, yayin da yake wucewa ta mashigar Hurmuz.

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar kwanaki biyu da suka gabata, cewa gwamnatinsa ta sanar da bangaren Iran a hukumance cewa yarjejeniyar tsagaita wuta ta ƙare, yana nuni da cewa "tattaunawar za ta ci gaba."

................

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha